Magungunan infection na da yawa. A wannan rubutun zamu kawo muku magungunan Infection na gargajiya.
- Yogurt da Zuma: Yogurt da zuma ana iya hadasu a sha dan magance matsalar Infection, ana kuma iya samun Yogurt din wanda bai da suga ko wanda aka hada a gida a hada da zuba a shafa a gaban mace, kada a tura ciki,shima yana maganin infection sosai.
- Man kwakwa: Man Kwakwa na da matukar tasiri sosai wajan magance matsalar Infection musamman wanda yake sa yawan kaikai, yanda ake yi shine kawai a samu man kwakwa sai a shafa a gaban mace, ana iya yin hakan sau daya kullun har a samu sauki.
- Saka Tsumma Me sanyi: A samu ruwan sanyi a samu tsumma me tsafta a sakashi a ciki, sai a dora akan gaban mace. Hakan baya maganin infection amma yana sanyawa a samu saukin kaikayi da infection ke sawa.
- Tafarnuwa: Akwai bayanan dake cewa saka Tafarnuwa a cikin farji yana maganin Infection. Hakanan ana iya rika saka tafarnuwa a cikin abinci a rika ci.
- A kiyaye a daina saka pant wanda ya matse, saka Panta wanda ya matse yana taimakawa wajan kamuwa da cutar infection hakanan yana da kyau a rika bacci babu pant dan samun iska da kyau.
- Shan Vitamin C: Shan Vitamin C yana taimakawa matuka wajan magance matsalar infection, idan ba’a samu Vitamin C ba ana iya rika shan Lemu.
Yaya cutar Infection take?
Cutar infection wata cuta ce dake saka kaikai ko kumburi ko fitar ruwa me zafi ta gaban mace ko namiji. Duka wadannan alamu na iya haduwar wa mutum ko kuma guda daya.
Za’a iya kuma ganin kuraje a gaba, ko jin zafi yayin fitsari da jin zafi yayin jima’i.
Abubuwan dake kawo cutar infection sun hada da Jima’i musamman da mutane barkatai, Masu cutar kanjamau ko cuta me karya garkuwar jiki na iya fama da Infection, Ciwon suga, Shan magungunan Antibiotics, daukar ciki, Jinin Al’ada, yawan shekaru.
Allah ya sauwake.