Yadda Mala’iku Suka Kai Ni Aljannah Har Na Gana Da Tsohon Abokina Kafin Na Dawo, Inji Godwin Ugeelu Bayan Gawarsa Ta Miƙe A Jihar Nassarawa.

Godwin Ugeelu, wani mai maganin gargajiya mazaunin Jihar Nasarawa ya farka ya fito daga akwatin gawa kwana biyu bayan mutuwarsa a ranar da za a birne shi.
Daga bisani, Ugeelu ya bada labarin dukkan abin da ya gano a yayin da aka kai shi ‘Aljanna’ da kuma dalilin da yasa Ubangiji ya bashi damar dawowa duniya.
Godwin Ugeelu ya ce:
“Na gode wa Ubangiji da ya sake bani wata rayuwar bayan ɗanɗana mutuwa. Abin ala’jabi ne yadda Allah ya sake bani wata damar rayuwa don in bauta masa in kuma yadda sakonsa.”
“Tafiya ta zuwa Aljanna mai sauƙi ne. Na ruɗe kan abin da Ubangiji ya min. Abin da zan iya tunawa shine mantuwa ta kama ni lokacin da na ke rashin lafiya, amma daga baya mutane suka taru a ƙauyen mu don zaman makoki na.”
“Sararin samaniya ta bude kuma na ga wani abu tamkar babban na’urar satelite na gwal a sama. Ba zan iya sanin ko wannan ne Bible ke kira Aljanna ba, amma wani Mala’ika mai tsawon kafa 75 ya gaishe ni a ƙofar shiga.”
“Mala’ikan na rike da takobi na gwal kuma akwai wani abu a kansa kamar gashi na gwal. Na kuma ga wasu Mala’iku biyu a bayansa rike da littafai masu ɗauke da kalaman ubangiji.
“Mala’ikun uku sun tattauna na ƙanƙanin lokaci sannan daga baya suka bari na shiga birnin Aljanna.”
“Da shiga na birnin, na hadu da wani aboki na tun muna yara shekaru 22 da suka gabata. Sunansa Choko Aguma. Shine ya zagaya da ni birnin da kowa ke bautan Ubangiji.”
“Ya tambaye ni game da wasu mutane amma na fada masa ban san inda wasu suke ba, wasu kuma suna da rai amma wasu sun daɗe da mutuwa.” Inji Godwin