Tuesday, March 17
Shadow

‘Yan Bìndìga ne ke mulkar Najeriya>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ‘yan Bindiga ne ke mulkar Najeriya.

El-Rufai yace dan haka Najeriya na cikin tsaka mai wuya.

El-Rufai yace ‘yan Najeriya na ci gaba da maimaita kuskuren da suka yi a baya na zabar shuwagabannin da bana gari ba.

Ya bayyana hakane a babban birnin tarayya, Abuja ranar Asabar a wajan wani taro.

Yace Najeriya na cikin matsalar da bata taba shiga ba tun shekarar 1914 a yayin sa aka hade Arewa da kudu.

Yace mafi yawancin shuwagabannin basu san yanda zasu gudanar da mulki ba kawai su dai su samu mulkin shine a gabansu.

Karanta Wannan  Ni ba irin sakarkarun 'yan siyasar nan bane wanda kawai daga an musu zargin karya sai su sauka daga mukaminsu, Ni ba zan sauka daga kan mukami na ba>>Godswill Akpabio

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *