
Majalisar wakilai ta bayyana cewa alamu na kara fitowa fili dake nuna mayakan Kungiyar Bòkò Hàràm sun fi sojojin Najeriya makamai masu kyau.
Majalisar ta bayyana hakane a zamanta na ranar Talata inda ta bayyana damuwa matuka kan harin da ake zargin kungiyar ta Boko Hàràm da kaiwa a barikin sojoji ta Giwa dake jihar Borno.
Majalisar tace wannan alamace karara dake nuna cewa mayakan kungiyar ta Bòkò Hàràm sun fi sojojin Najeriya makamai masu kyau.
‘yan majalisar sun kuma bayyana damuwa kan yanda kungiyar ke dawowa a hankali da kuma asarar rayukan da ake samu a hare-haren da take kaiwa a jihohin Borno da Yobe.
Duk da yawan kudin da gwamnati ke warewa bangaren tsaro na karuwa duk shekara, amma korafi na yawa a kan yawa ko ingancin makaman da ake siyowa sojojin.
Misali a shekarar 2023, Gwamnati ta ware Naira Tiriliyan N2.98 ga sojojin Najeriya, hakanan a shekarar 2024 Naira Tiriliyan N3.25 gwamnati ta warewa bangaren tsaro, inda a shekarar 2025 kuma Naira Tiriliyan N4.91tn gwamnatin ta warewa bangaren na tsaro.
Saidai duk da haka Najeriya tana ci gaba da fama da matsalar tsaro data hada da ta masu garkuwa da mutane da sauransu.