
Kungiyar masu sana’ar kiwon kaji sun koka da rashin kasuwar kwan kajin inda suka ce hakan ya farune saboda tsadar rayuwa a tsakanin al’umma.
Shugaban kungiyar reshen jihar Jigawa, Mr. Hussaini Gumelne ya bayyana hakan yayin da suka kaiwa Gwamnan jihar, Umar Namadi ziyara.
Yace sun fara ganin kasuwar Kwan ta yi kasa ne tun bayan da aka cire tallafin man fetur. Inda yace ‘yan Najeriya da yawa a yanzu basa iya cin kwai.
Ya nemi cewa, Gwamnati ta basu tallafi ta hanyar baiwa membobinsu musamman mata horaswa sannan Gwamnatin ta saka Kwai cikin shirin ta na ciyar da dalibai ta yanda zasu rika samun ana sayen kwan a hannunsu.