
Majlisar tarayya ta shigar da kara inda take kalubalantar Gwamnonin PDP 11 da suka shigar da kara suna neman a Tursasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya janye dakatarwar da yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
Majalisar tace Kotun ma bata da hurumin sauraren wannan karar.
Sannan ta nemi kotun ta sa Gwamnonin PDP din su biya majalisar Naira Biliyan 1 saboda shigar da wanan karar da ta sabawa doka.
Gwamnonin PDP da suka shigar da karar sune Gwamnonin jihohin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara, da Bayelsa.
Sun bayyana cewa shugaban kasa bashi da hurumin shiga harkar zababben gwamna da mataimakinsa ko ya saukesu ya maye gurbinsu da wasu wanda ba zababbu, hakanan shugaban bashi da hurumin dakatar da majalisar jihar.
Hakanan sun ce majalisa bata da hurumin amincewa da bukatar shugaban kasa ta dakatar da gwamnan ta hayar sauraren murya irin su WhatsApp dole sai ‘yan majalisar suna bayyane a zahiri.
Dan hakane suke neman kotu ta warware musu matsalar da bayyana musu ko shugaban kasa da majalisarsa na da hurumin shiga harkar jiha.