Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi holen wata matashiya mai suna Shamsiyya da ake zargi da ƙwarewa wajen satar wayoyi a unguwanni daban-daban a Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Abudullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kama Shamsiyya ne ranar 21 ga watan Disamba bayan shafe tsawon shekara guda ana farautar ta.
”Shamsiyya ta ƙware wajen ɓullo da dabarun yaudara daban-daban don hilatar mutane wajen sace musu wayoyi”, in ji sanarwar.
Kiyawa ya ƙara da cewa wadda ake zargin kan yi aiki ne tare da wasu mutu huɗu da ke taimaka mata ciki har da ɗan adaidaita sahu da ƙwararre wajen cire wayoyi daga makulli, wajen gudanar da ayyukanta.
”Ƙwararriyar mai yaudara ce da ke shiga gidajen matan aure tare da sace musu wayoyinsu da kuma yin amfani da wayoyin wajen sace musu kuɗaɗen daga asusun ajiyarsu na banki”, in ji SP Kiyawa.