Sunday, March 23
Shadow

YANZU YANZU: An Binciko yadda Nuhu Ribaɗu yayi Awun gaba da wasu Biliyoyin kuɗaɗe a lokacin da yake shugaban Hukumar EFCC, inji Fitaccen mai Binciken nan Dr. Idris

Nasan wanda yake Sauyawa Nuhu Ribaɗu Dalar Amurka na cin hanci da rashawa.

Fitaccen mai bincike kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a ɗan asalin Najeriya, mazaunin kasar Ingila, Dr. Idris Ahmed ya bayyana wasu muhimman zarge-zarge da ya sani akan Malam Nuhu Ribadu mai taimakawa Shugaban kasa kan sha’anin tsaron Najeriya.

Dr. Idris ya bayyana cewa, “A lokacin da yake shugaban hukumar EFCC, ya karbi makudan kudaden cin hanci. Musammab dalar Amurka, akwai wani wanda Shi ne me yiwa Nuhu Ribadu canjin dalar Amurka, wanda tsohon dan sanda, ne ACP mai ritaya ne ana kiransa da suna (retired) Rabiu Abubakar Shariff.

Karanta Wannan  Jadawalin masu kudin da suka bayar da tallafi ga wanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno

Rabiu Abubakar Shariff shi clasmate dina ne lokacin muna karatun sakandare. Shine wadda Lieutenant General Tukur Buratai ya turo shi zuwa kasar Burtaniya, domin ya saci salulata. Wanda Bai yi nasaran yin hakan ba Har Allah ya tona masa asiri. amma sunyi nasaran hacking salulan daga bisani.

A lokacin da Rabiu yake canjawa Ribadu kudi a kasuwan canjin dollar dake Obalande Lagos, yana zaune ne a boys quarter na gidan babban yayanmu, marigayi injiniya, Ahmed, a Victoria Island, dake Legas,

Wannan shi yasa nake da cikakken bayani game da jagwal da Malam Nuhu Ribadu yayi da Rabiu Abubakar Shariff mai canjin dala.

Yanzu haka da muke magana, Rabiu Abubakar Shariff shine mai baiwa Nuhu Ribadu shawara akan tsaro!

Karanta Wannan  Ban Taba Zuwa Gidan Sadiya Haruna Ba, Bare Har Na Ci Abinci Tare Da Yin Bacci A Gidanta, Cewar Alkalin Da Ya Yanke Mata Hukuncin Watanni Shida A Gidan Yari

Jama’a, da irin wannan shugaban kasan, da NSO nashi, da mai baiwa NSO shawara akan tsaro, ta ina ne Najeriya zata ci gaba? Dukkansu ukun azzalumai ne, maciya amanan Najeriya da al’ummanta. Inji Dr. Idris Ahmad.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *