
Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a tsawon mulkin da ya yi shekara takwas, ko sake fentin gida bai yi ba .
Buhari ya faɗi haka ne a lokacin da ƙungiyar ƴan jarida reshen kafofin yaɗa labarai a Katsina suka kai masa ziyara a gidansa dake garin Daura.
Ya ce yana cikin ƙoshin lafiya idan aka kwatanta shi da abokansa da suka taso tun suna yara, inda wasu daga cikinsu da sanda suke dogarawa su yi tafiya.
Ya kuma ce Mataimakin Shugaban ƙasa, kashin Shattima ne ya fidda kuɗi daga aljihunsa ya ke gyara masa gidansa na Kaduna.
“Da zarar an kammala gyaran gidan zan koma kaduna”, inji Buhari.
Tunda da farko, shugaban tawagar ƴan jaridun, Yusuf Ibrahim Jargaba ya faɗa wa tsohon shugaban ƙasar cewa sun kawo masa ziyarar ban girma ne da kuma yi masa ban gajiya.
Jargaba ya nuna jin-daɗinsa ganin yadda ya ga Muhammadu Buhari cikin ƙoshin lafiya.
Ya kuma yi masa addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.