Friday, December 5
Shadow

YANZU-YANZU: Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Ya Amince Da Naɗin Dakta Asiya Balaraba Ganduje A Matsayin Darakta A Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

A wani mataki na duba cancanta da ƙwazon aiki, shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da naɗin Dakta Asiya Abdullahi Umar Ganduje a matsayin daraktar sashen kula da al’umma da raya yankunan karkara a sabuwar hukumar raya yankin Arewa maso Yamma.

Naɗin Dakta Asiya Ganduje a wannan matsayi ajiye ƙwarya ne a gurbinta duba da cewa mace ce jaruma mai juriya da himmar aiki. Ta daɗe tana ɗawainiya da hidimtawa al’umma ta fannoni daban-daban na rayuwa daga aljihunta. Ta ba da gagrumar gudunmawa wajen raya ilimi na addini da na zamani a birane da karkara. Ta taimaki ɗumbin jama’a da tallafin karatu, aikin yi, sana’o’in dogaro da kai da harkokin kula da kiwon lafiya da ayyukan jinƙai.

Karanta Wannan  ZABEN 2027: Ba Muśĺim-Mùšĺìm Bà, Ko Mùmìñi-Mùmìñi Ne Ba Za Mu Zaba Ba, Inji Wani Fusataccen Ĺimàmi, Malam Abubakar Mai Imani

Dakta Asiya Ganduje ba a iya nan ta tsaya ba, mace ce mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira. Ko da lokacin da mahaifinta yake matsayin gwamnan Jihar Kano ta yi amfani da ƙwarewarta ta fannoni daban-daban ta tallafa masa wajen samun nasarar lashe zaɓe. Ta ja mutane da dama a jiki ta taimake su wanda hakan ya ƙarawa mahaifinta da gwamnatinsa farin jini.

Ba ta wannan matsayi na darakta a hukumar raya yankin Arewa maso Yamma a yanzu, gagarumin cigaba ne ga Arewa da ma Najeriya gaba ɗaya. Domin kuwa ayyukan da aka kafa hukumar domin su tuni dama can ita ta yi nisa wajen gudanar da ire-irensu wanda wannan matsayi zai ƙara mata himma ne da cigaba da faɗaɗa alkhairanta su game ko’ina.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya sa a janye 'yansanda daga tsaron manyan mutane a kasarnan, yace duk wani babban mutum dake neman tsaro a bashi jami'an Civil Defence

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *