
Dansandan Najeriya a Ofishin ‘yansandan dake Mada jihar Nasarawa ya harbi kanshi ya kashe kansa.
Rahotanni sunce a ranar da ya kashe kansa, anga dansandan me suna Dogara Akolo-Moses yana yawo abinsa.
Shaidu sun ce ya shiga wani daki ne ya kulle ya harbi kansa a cikin ofishinsu, kuma karar harbin da abokan aikinsa suka ji ne yasa suka ruga da gudu zuwa cikin dakin da yake.
Nan take suka iskeshi kwance a cikin jini.
Zuwa yanzu dai ba’a san dalilin da yasa ya kashe kansa ba.
Kakakin ‘yansandan jihar, Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ana kan bincike.