
Malam Isa Ali Pantami ya jaddada wa jagorancin Darul Hadith cewa, dole su zauna da dukkan daliban Malam Albaniy da suka kora daga Darul Jadith ayi sulhu a samu mafita, idan ba haka ba Malam yace da kansa zai jagoranci gurfanar dasu a Kotu har zuwa Supreme Court zai dauki nauyin shari’ah.
Sannan Malam Isa Ali Pantami ya tabbatar da case din Aisha ‘yar Malam Albaniy wacce aka damfareta kudi Kimanin Naira Miliyan 10, ta biya Miliyan 5 ya rage saura Miliyan 5, mun nema mata taimako ta account dinta na Stanbic IBTC, kuma jama’a kun hada mata kudi kimanin Naira Miliyan 2 da dubu dari uku da wani abu kamar yadda zaku gani a hoto.
To nan take Malam Isa Ali Pantami a gurin da ya jagoranci zama dasu ya sa PA dinsa ya tura wa Aisha sauran kudi Naira Miliyan 3 da dubu dari uku ta account dinta na First Bank kamar yadda zaku gani a hoto.
Daga Comr Abba Sani Pantami a