Wata kungiyar Matasan Arewa Masu goyon Bayan Bola Tinubu Wadda take da yawan Mabiya miliyan 100 ta yiwa Shugaban ƙasa Bola Tinubu Alƙawarin kawo Masa Miliyoyin kuri’un Matasan Arewa a kakar zaɓe Mai zuwa ta 2027.

Wata ƙungiyar matasa masu rajin goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ake kira City Boy Movement ta sha alwashin tara ƙuri’u fiye da miliyan biyar daga matasa domin tallafawa sake tsayawar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 mai zuwa.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar, Mista Francis Shoga, ne ya bayyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Litinin a Maryland, Ikeja, jihar Lagos, wanda aka shirya domin fayyace manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu ga matasan Najeriya.

“Manufarmu a bayyane take – Muna son wayar da kan matasa tare da ƙarfafa musu gwiwa su fahimci gagarumin aikin da Shugaba Tinubu ke yi wajen farfaɗo da ƙasar nan. Zuwa 2027, za mu gabatar da ƙuri’un matasa miliyan biyar ba” in ji Shoga