Sunday, March 23
Shadow

Abubuwan da ya kamata ka sani game da komawar El-Rufai SDP

A jiya ne tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana komawa Jam’iyyar SDP inda yace ya fita daga Jam’iyyar APC.

A takardar barin APC da ya aikewa ofishin Jam’iyyar ya bayyana banbantar ra’ayi wanda yace ya gano ba zasu samu jituwa ba shi da Jam’iyyar ta APC.

Yace a baya yana da niyyar saidai idan ya daina siyasa ne zai daina yin Jam’iyyar ta APC amma a yanzu saboda kaucewa tsari da banbancin ra’ayi, yace ya bar Jam’iyyar duk da yana daya daga cikin wanda suka kafata.

El-Rufai yace babban abinda zai mayar da hankali a yanzu shine hado kan ‘yan Adawa dan su hade su kayar da Jam’iyya me mulki zabe a shekarar 2027.

Karanta Wannan  Alamomin mace mai dadi

Saidai a martanin da fadar shugaban kasa ta mayarwa da El-Rufai ta hannun ms baiwa shugaban kasar shawara a fannin sadarwa, Daniel Bwala yace zasu saka ido akan El-Rufai.

Yace ba matsala bace komawarsa wata Jam’iyya, amma ikirarin da yake na cewa zai mayar da hankali wajan ganin gwamnati me ci ta fadi zabe zai sa su saka ido akansa.

Yace amma ba zai yi nasara akan wannan aniya tasa ba.

Itama Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta bakin sakatarenta, Yahaya Baba-Pate tace bata damu da komawar El-Rufai SDP ba.

Tace yanzu abinda ke gabanta shine na tabbatar da Gwamna Uba Sani da Bola Ahmad Tinubu sun zarce a shekarar 2027.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya nemi Gwamnatin tarayya ta bashi dama zai iya kawo ƙárshéɲ rikíciɲ Fulani a Nájeríya wanda shine ya jawò matsalar gárkúwa da mutane a ƙasar

Jam’iyyar tace akwai manyan mutane ‘yan Adawa dake komawa cikinta dan haka fitar El-Rufai daga cikinta ba zai sa ta cikin damuwa ba.

Shima da yake mayar da martani kan lamarin, tsohon Sanatan kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani yace ba abin damuwa bane dan El-Rufai ya fita daga APC dan kuwa dama a yanzu bashi da wani karfi a siyasance.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zasu zarce a mukaminsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *