Monday, December 16
Shadow

Yawan man fetur din da Najeriya take hakowa ya ragu

Bayanai daga babban bankin Najeriya sun nuna cewa yawan man fetur din da Najeriya ke hakowa ya ragu a watanni 3 na biyu na shekarar 2024.

Man fetur din da Najeriya ke hakowa ya ragu da kaso 4.51% cikin 100 inda a yanzu Najeriya ke hako ganga Miliyan 1.27 a duk rana.

A watanni 3 na farkon shekarar 2024 kuwa, Najeriya na hako ganga miliyan 1.33 ne wanda hakan ke nuna cewa an samu koma baya kenan.

An dora alhakin hakan akan satar danyen man da kuma lalata bututun man fetur din wasu bata gari ke yi a yankin Naija Delta.

Hakanan yawan man fetur din da Najeriyar ke hakowa yayi kasa da yawan wanda kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta bukaci kowace kasa ta rika hakowa watau Ganga Miliyan 1.58 a duk rana.

Karanta Wannan  Maraba Da Watan Mauludin Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam! Ya Allàh Ka Hore Mana Watan Máụludi Da Abun da Ya Ƙunsa, Ka Buɗe Mana Manyan Taskoki Na Arziƙi Domin Mu Yi Hidima Cikin Wànnan Watan Mai Albarka, Cewar Ɗan Ƙasar Chana, Masanin Hausa, Malam Murtala Zhang

Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL dai ya sanar da cewa ya kashe Naira Biliyan N62 wajan kula da bututun man fetur din

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *