A yayin da aka fara zàngà-zàngà akan yunwa a yau, farashin kayan abinci ya sake tashi a kasuwannin Najeriya.
Hakan ya farune yayin da mutane ke ta rububin ahuga kasuwa dan sayen kayan abinci saboda rashin sanin me zai je ya dawo game da maganar zanga-zangar.
Gwamnatin tarayya dai ta yi iya bakin kokarinta dan ganin ba’a yi zanga-zangar ba amma abun ya ci tura inda tuni an fara zanga-zangar a jihohi da yawa na kasar nan.