Thursday, December 25
Shadow

Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci

Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci.

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage ranar yanke hukunci kan shahararriyar ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, har zuwa ranar 20 ga watan Mayu, bayan da masu gabatar da kara su ka nemi izini don gyara tuhumar da a ke yi mata.

Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Murja da tuhuma daya tak kan zargin cin zarafin Naira.

An ga Murja a wani faifen bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta tana watsar da kudi har Naira 400,000 tare da rawa a lokacin wani biki da aka gudanar a otal din Tahir Guest Palace a watan Disamba na shekarar 2024.

Karanta Wannan  'Yan Bindiga sun shiga uku, An kai jami'an 'yansanda na musamman da suka kware da yaki da 'yan Bìndìgà a kowace jiha a kasarnan>>IGP

Tuni dai wanda ake tuhumar ta amsa laifin da ake zarginta da shi.

A zaman kotun na ranar Talata da aka tsara domin yanke hukunci, lauyan EFCC, Musa Isa, ya nemi izinin gyara tuhumar, wanda lauyan dake kare wacce ake tuhuma, Abubakar Saka, ya ki amincewa da shi.

Saka ya ce gyaran tuhumar zai iya jinkirta shari’ar kuma ya shafi hakkin wadda ake tuhuma na samun adalci.

Ya kuma bayyana cewa tawagar lauyoyin kare Murja na bukatar isasshen lokaci domin nazarin sabon tuhumar.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Simon Amobeda, ya amince da bukatar masu gabatar da kara, sannan ya dage cigaban shari’ar har zuwa 20 ga watan Mayu.

Karanta Wannan  An sace jakar shugabar hukumar tusaron kasar Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *