Tuesday, September 22
Shadow

An bayyana dalilin da yasa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima har yanzu bai koma Gidan da Gwamnati ta gina masa ba a Abuja akan Naira Biliyan 22

Rahotanni sun ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima har yanzu bai koma gidan da gwamnati ta gina masa ba na Naira Biliyan 22

Rahotanni na jaridar Leadership yace Ma’aikatar Babban birnin tarayya Abuja, FCTA tuni ta kammala ginin gidan ta kuma mikawa Gwamnatin tarayya shi, kuma Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar dashi.

Saidai har yanzu mataimakin shugaban kasar bai koma ciki da zama ba.

Har yanzu Kashim Shettima na zaune a cikin fadar shugaban kasa.

Rahoton yace ana zargin matsalar tsaro ce ta jawo hakan.

Sannan akwai wasu zarge-zarge a kafafen sada zumunta dake cewa rashin komawar Kashim Shettima sabon gidan nasa, ya komane ya tarar an dasa Kyamarorin leken Asiri dalili kenan da yasa ya fita daga gidan

Karanta Wannan  Naira Biliyan N39bn d aka kashe wajan gyaran babban dakin taro na Abuja wanda aka sakawa sunan shugaban Tinubu, kudin zasu iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan makarantu 1,200

Saidai rahotan yace maganar gaskiya Kashim Shettima bai koma gidan nasa da aka gina masa ba, Asalima wani hadiminsa ya karyata wannan zargi.

Har yanzu dai a hukumance babu wani dalili da aka bayar na kin komawar Kashim Shettima gidan.

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne ya bayar da kwangilar gina gidan amma ba’a yi ba sai a zamanin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *