Friday, December 5
Shadow

Zuwa yanzu, Ahmed Musa ne kadai ya cika alkawarin da yayi na bayar da gudummawar Naira Miliyan 5 a wajan Bikin Tauraron Kannywood, Jamilu Kochila, kalli Rasit

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa shine na daya wajan cika Alkawarin gudummawar kudi a wajan bikin tauraron Kannywood, Jamilu Kochila.

Ahmed Musa, yayi alkawrin bayar da Naira Miliyan 5.

Kuma a jiya, Mansurah Isah ta wallafa Rasit din shaidar cika alkawarin da yayi.

Mansurah ta kara da cewa zasu fara wallafa sunan wadanda suka cika Alkawarin da suka dauka.

Saidai itama Sadiya Kabala ta bayyana cewa, Daga yanzu idan aka je wajan Biki zata tashi tace ta bada gummawar Naira kaza sai ta yi fuska kawai.

Hakan dai alamu ce dake nuna cewa, da yawa basu cika alkawuran da suka dauka a wajan bikin ba.

Karanta Wannan  Kalli sabon Bidiyon Mansurah Isah da ya jawo cece-kuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *