Tuesday, October 6
Shadow
Kalli Bidiyon: Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu na shan yabo saboda shiga cikin talakawa ana yakin neman zaben babansa dashi

Kalli Bidiyon: Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu na shan yabo saboda shiga cikin talakawa ana yakin neman zaben babansa dashi

Duk Labarai
Dan gidan shugaban kasa, Seyi Tinubu na ta shan yabo saboda yanda yake shiga cikin talakawa ana yiwa mahaifinsa yakin neman zabe. A jiya, An ga Seyi Tinubu a titin lagos tare da talakawa yanawa Mahaifinsa yakin neman zabe. Da yawa na cewa, Shine dan shugaban kasa na farko daya fito ana yiwa mahaifinsa yakin neman zabe dashi. Yayin da abinda aka saba shine 'ya'yan 'yan siyasar basa ma Najeriya yayin da ake yakin neman zabensu. https://twitter.com/abdullahayofel/status/2106810728812261862
Kalli Bidiyon: Yanda aka kunyata dan majalisa, Alhassan Ado Doguwa, Ya rika fadin Najeriya, Wasu na cewa sai Atiku wasu na cewa sai Tinubu

Kalli Bidiyon: Yanda aka kunyata dan majalisa, Alhassan Ado Doguwa, Ya rika fadin Najeriya, Wasu na cewa sai Atiku wasu na cewa sai Tinubu

Duk Labarai
Bidiyon dan majalisa daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa ya dauki hankula bayan da ya rika fadar Najeriya wasu na ce masa sai Atiku wasu na ce masa sai Tinubu. Da ya dan yi muzurai, da ya kara cewa Najeriya aka ce masa sai baba. A karshe dai yace baya son a rika raba masa hankali, shi bai san wani Baba ba Tinubu ya sani. https://twitter.com/KafinHausaa/status/2107021753402716402
Kalli Bidiyon: Rahotanni na cewa Gfresh Al-Amin ya saki matarsa, Sadiya Haruna

Kalli Bidiyon: Rahotanni na cewa Gfresh Al-Amin ya saki matarsa, Sadiya Haruna

Duk Labarai
Rahotanni a kafafen sada zumunta na ta yawo cewa, Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin Ya saki matarsa, Sadiya Haruna a kasar Saudiyya. Gfresh dai da Sadiya sun je Saudiyya Aikin Umrah inda rahotanni a kafafen sada zumunta ke cewa Sadiyar ta kamashi yana wayane da tsohuwar matarsa, Maryam Nicki Minaj, Abinda ya hadasu fada kenan har ya saketa. https://www.tiktok.com/@peoplene5/video/7693027584224890130?_r=1&_t=ZN-9AIRI3LqlOw Zuwa yanzu dai basu tabbatar da wannan magana ba. https://www.tiktok.com/@mrs_sameer7/video/7692925941068139828?_r=1&_t=ZN-9AIRhrR1TDq
Kalli Bidiyon: Ya aika matarsa kasar Canada, ta yi Blocking dinsa

Kalli Bidiyon: Ya aika matarsa kasar Canada, ta yi Blocking dinsa

Duk Labarai
Ni ma'aikacin bankine. Na nema kuma na samu damar zama a kasar Canada ni da iyalina. Na ajiye aikin bankin da nake yi dan mutafi can ni da matata da yarana. Saidai bankin sun ce sai na jira an yi bincike kan ofis din dana rike. Dan haka ne na fara aika matata da yarana Kasar Canada dan kada damar ta wucemu. Ko da matata ta isa kasar Canada da 'ya'yana sai ta yi Blocking dina bana iya kiranta, sannan ta hana yarana magana dani. Dama Tun kamin ta tafi akwai cin amanata da take yi da wasu mazan, amma na yi tsammanin idan muka je kasar Canada inda bata san kowa ba zata canja. Inji Magidanci Mr Francis Ushie Ya bayyana cewa a yanzu yana tunanin zai mikawa ofishin jakadancin kasar Canada da korafi kan abinda matar tasa ta mai. Sannan kuma yace duk da abinda ta mai, har...