Sunday, March 23
Shadow

Ƴan bìndìgà sun sace wanda ya lashe gasar karatun al-Qur’ani ta Najeriya

Ƴan bìndìgà sun sace mutumin da ya zama zakaran gasar karatun al’qur’ani ta bana tare da danginsa a kan hanyar Faskari zuwa ƴankara a jihar Katsina.

Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Hon Musa Ado Faskari ya shaida wa BBC faruwar lamarin, inda ya ce ƴanbindigar sun sace Abdulsalam Rabi’u Faskari tare da mahaifinsa da ƴan’uwansa a lokacin da suke kan hanyar komawa gida bayan sun halarci fadar gwamnatin Katsina inda gwamna ya karrama gwarzon.

Hon. Musa Faskari ya ce gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ne ya gayyaci , Abdulsalam Rabi’u Faskari tare da iyalansa ciki har da mahaifinsa a ƴan’uwansa, domin karrama shi bisa nasarar da ya samu ta zama gwarzon gasar karatun al-qur’ani da aka kammala a jihar Kebbi.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya Christopher Musa Ya Ziyarci Ƙasar Nijar.

”A kan hanyarsu ta komawa gida ne, sun baro Funtua a kan hanyar Faskari zuwa ƴankara , ƴanbindiga suka tare su tare da yin garkuwa su duka, sai mutum guda da ya samu nasarar kuɓuta”, in ji shugaban ƙaramar hukumar.

Ya ce lamarin ya rutsa da aƙalla mutum bakwai – waɗanda duka dangin juna ne, sai abokin gwarzon gasar guda, wanda shi ma ya halarci taron karramawar.

Ya ƙara da cewa hukumomi na ci gaba da neman mutanen domin kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *