Saturday, June 27
Shadow

Da Duminsa: Wajan taron Rainbow da muka shirya yin babban taron mu na kasa a yau, yace ya fasa bamu wajan saboda Gwamnati ta masa barazanar kwace lasisinsa idan ya bamu>>Inji Jam’iyyar ADC

Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa wajan taro na Rainbow data shirya yin taronta na kasa a yau, Talata ya sanar da ita cewa ya fasa bata wajan.

Me magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa inda yace, Rainbow ya basu dalilin cewa, Hukumar kula da babban birnin tarayya, Abuja, FCTA ce ta musu barazanar cewa idan suka bayar da wajan za’a kwace lasisinsu.

Saidai Bolaji Abdullahi yace sun riga sun sakawa takardar yarjejeniya da raibow hannu dan haka ba zasu fasa ba a wajan zasu yi taronsu.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kalli yanda Matan Jihar Rivers suka tashi suka kama gabansu yayin da ake tsaka da taro matar shugaban kasa, Remi Tinubu na jawabi, sun ce basa son jin jawabinta, Ance bai kamata su kunyata matar shugaban kasar irin haka ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *