Monday, December 9
Shadow

Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu’amulla da bankuna – CBN

Babban Bankin Najeriya ya ce akwai ‘yan ƙasar sama da miliyan 28 da ba su da hanyoyin mu’amulla da banki – yawancinsu kuma suna yankuna ne na karkara.

Mataimakin gwamman bankin mai kula da fannin hada-hadar kuɗi, Philip Ikeazor, wanda ya bayyana haka jiya Talata, ya ce, bankin da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki tuƙuru domin rage wannanan matsala ta yadda za a samar da hanyoyin mu’amulla da bankuna da jama’a.

Ya ce, alƙaluma sun nuna waɗanda ke cikin wannan rukuni na waɗanda ba su da hanyar samun bankuna yawanci mata ne da matasa da al’ummomin karkara da masu ‘yan ƙanana da ƙanana da kuma matsakaitan sana’o’i.

Karanta Wannan  Mutane 243,000 sun daina biyan kudin talabijin ta DSTV a Najeriya saboda tsadar rayuwa

Mista Ikeazor, wanda ke magana a Lagos a wajen taron ƙasa da ƙasa na wannan shekara kan mu’amullar jama’a da bankuna ya ce, matakan da bankin yake ɗauka ne ma ya sa aka samu raguwar mutanen da ba sa mu’amulla da bankunan daga kashi 46.3 a 2010, zuwa kashi 26 cikin ɗari a wannan shekara – wanda shi ne sama da mutum miliyan 28.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *