Wednesday, January 8
Shadow

‘Ƙungiyar su Shekarau za ta koma jam’iyyar siyasa’

Ƙungiyar League of Northern Democrats (LND) wadda wasu ƴan siyasa daga arewacin Najeriya suka kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ta fara yunƙurin zama jam’iyyar siyasa domin fuskantar zaɓen shekarar 2027.

Ƙungiyar ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da gazawa wajen ciyar da Naeriya gaba, sannan ta buƙaci ƙungiyoyin kudancin ƙasar da su shigo su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ceton ƙasar.

A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar, Dr Umar Arɗo, ya ce ƙungiyar ta LND za ta kawo sauyi tare da sake dawo da martabar ƙasar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda 'yansanda suka bi sahun farar hula suka tsere yayin da bata gari suka sace akwatin zabe a wata mazaba dake jihar Ondo

Ya ce rashin ingancin gwamnati ne ya jefa ƙasar cikin ƙangin talauci da rashin tsaro da rashin tabbas.

Sai dai tuni jam’iyyar APC ta mayar da martani, inda daraktan watsa labaranta, Alhaji Bala Ibrahim ya ce su dai ko gezau, domin a cewarsa, rikiɗewar ƙungiyar zuwa jam’iyyar siyasa ba barazana ba ce ga jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *