Ƴan majalisar wakilai 50 sun buƙaci a sako Nnamdi Kanu, sun aike da takarda ga Tinubu
Kimanin ƴan majalisar wakilai 50 daga sassa daban-daban na Najeriya da jam’iyyun siyasa, wadanda aka fi sani da ‘Concerned Federal Lawmakers for Peace and Security in South East’, sun roki shugaba Bola Tinubu da ya yi amfani da sashe na 174 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, 1999 (kamar yadda gyara) da kuma sashe na 107 (1) na dokar shari’a ta 2015 domin sakin jagoran ‘yan asalin yankin Biyafara, Nnamdi Kanu daga tsare shi don taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a yankin kudu maso gabas.
Ƴan majalisar, wadanda suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban da kuma shiyyoyin siyasa a fadin kasar nan, sun kuma yi kira ga shugaba Tinubu da ya fara shirin zaman lafiyar shugaban kasa domin magance duk wasu matsaloli da kalubalen da ke addabar yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai shafi uku da ‘yan majalisar suka sanya wa hannu, mai kwanan wata 19 ga watan Yuni, 2024, da kuma aikewa da shugaban kasa.
Wadanda suka sanya hannu sun hada da Hon Obi Aguocha (Abia), Hon Ikenga Ugochinyere (Imo), Hon. Aliyu Mustapha (Kaduna), Hon Midala Balami (Borno), Hon Afam Ogene (Anambra), Hon. Abiante Awaji-Inombek (Rivers), Hon Dominic Okafor (Anambra), Hon Etanabene Benedict (Delta), Hon. Shehu Dalhatu (Katsina), Hon Chinedu Emeka Martins (Imo), Hon. Matthew Nwogu (Imo), Hon. Muhammed Buba Jagere (Yobe), Hon Peter Aniekwe (Anambra), Hon Koki Sagir (Kano), Hon Amobi Oga (Abia), Hon Gwacham Chinwe (Anambra), Hon. Uchenna Okonkwo (Anambra), Hon. Abdulmaleek Danga (Kogi), Hon. Osi Nkemkama (Ebonyi), da sauransu.
Sun bukaci shugaban kasar da ya umurci babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi SAN, da ya yi amfani da ikonsa a karkashin tanadin sashe na 174(1) na kundin tsarin mulki da sashe na 107(1) na kundin tsarin mulkin kasa.