Sunday, March 16
Shadow

Ƴansanda sun kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa a Bauchi

Rundunar ƴansanda a jihar Bauchi ta ce ta kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, CSP Ahmed Wakili ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne ranar 24 ga watan Fabrairu a wata unguwa mai suna Abujan Kwata.

Ya ce ana zargin matashin mai suna Safiyanu Dalhatu ɗan shekara 20, da amfani da taɓarya wajen lakaɗawa mahaifiyarsa duka har ta kai ga mutuwarta.

“Matashin ya yi wa mahaifiyar tasa mai suna Salama Abdullahi mai shekara 40 munanan raunuka a hannu kuma ya yi mata jina-jina abin da ya kai ga mutuwarta,” in ji sanarwar ƴansandan.

Karanta Wannan  Da Duminsa: An sake Samun Fashewar Tankar Man Fetur A Jihar Jigawa

CSP Wakili ya ce bayan samun rahoton abin da faru ne suka aika tawagar jami’ansu zuwa anguwar, inda suka ɗauki mahaifiyar matashin zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa – inda wani likita ya tabbatar da mutuwarta.

Ya ƙara da cewa suna riƙe da matashin a halin yanzu da kuma taɓaryar da ya yi amfani da ita domin ci gaba da bincike.

Ya ce bayan kammala bincike ne za su miƙa wanda ake zargin hannun kotu domin yanke masa hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *