Thursday, May 7
Shadow

Ɗan majalisa a Borno ya fashe da kuka inda ya roƙi a ba shi dama karo na biyar,ya cewa mutanen mazabarsa shi bawan Allah ne kuma talaka

Ɗan majalisa a Borno ya fashe da kuka inda ya roƙi a ba shi dama karo na biyar.

Ɗan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar mazabar Magumeri, Audu Mustapha Ganga, ya roƙi al’ummarsa da su amince da sake tsayawa takara karo na biyar.

Ganga, wanda ya shafe shekaru 16 yana kan kujera, ya fashe da kuka yayin da yake roƙon masu ruwa da tsaki da ke neman a sauya wakilci.

A cikin wani bidiyo da ya bazu, ya ce duk da matsin da ya fito daga ciki, ya yi ayyuka da dama ga al’umma, tare da alƙawarin yin ƙarin aiki idan aka sake zaɓensa.

Karanta Wannan  Ma'aikata ne suka yi yawa a jihar mu shiyasa muka kasa biyan mafi karancin Albashi na 70,000 inji Gwamnan Borno, Zulum

Rahotanni sun ce mutum shida sun riga sun sayi fom domin fafatawa da shi a zaɓen.

Sai dai wannan roƙo nasa ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon bayansa, yayin da wasu ke zargin cewa kukan na sa ba gaskiya ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *