Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton da Amnesty International ta fitar na zargin jami’anta da tsare tare da cin zarafin mata da yara da dama da suka tsere daga hannun ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.
Mai magana da yawun rundunar Edward Buba ta bakin mataimakinsa kan yaɗa labarai, Group Kaftin Ibrahim Ali Bukar, ya shaida wa BBC cewa “ba za su damu da irin waɗannan kalamai na son kai da aka yi da niyyar rage kwarin gwiwar sojojin fafutuka don tabbatar da tsaro ba”
Ya kara da cewa sojojin za su yi haɗin gwiwa mai inganci da Amnesty International idan akwai bukatar yin hakan kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kawar da ta’addanci da tabbatar da tsaro.
Wannan martanin ya zo ne kwana guda bayan da Amnesty International ta zargi gwamnati da gazawa wajen bai wa ‘yan matan tallafin da ya dace tare da sukar sojojin da tsare matan ba bisa ƙa’ida ba saboda alakarsu da mayakan Boko haram.
Rahoton ya yi iƙirarin cewa yawancin ‘yan mata sun fuskanci ƙarin cin zarafi na tsawon lokaci da sojojin suka tsare su ba bisa ƙa’ida ba, kuma an bar su a sansanonin gudun hijira.
A baya dai sojojin sun sha fuskantar zargin kashe-kashe ba bisa ƙa’ida ba, da kame ba bisa ƙa’ida ba, da kuma tilasta wa mata da yaran mata da aka ceto daga yankunan Boko Haram zubar da ciki.
A shekarar 2022, gwamnati ta yi wa labaran da ke nuna cewa sojojin kasar na gudanar da shirin zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba a yankin arewa maso gabas tun daga shekarar 2013 lakabi da labaran karya.