
Shugaban kungiyar shuwagabannin kananan hukumomi ta Najeriya kuma shugaban karamar hukumar Kaita, Bello Lawal ‘Yandaki wanda dan Jam’iyyar APC ne ya sha ehon bama so sannan aka koreshi daga kauyen ‘Yanhoho bayan da ya je yakin neman zabe.
Bello ya je yakin neman zabe ne a karo na biyu kauyen saidai ya gamu da fushin jama’ar yankin inda suka taru suka fasa masa gilasan mota sannan suka koreshi suna yi masa ihu.
A bidiyon da ya watsu sosai a kafafen sadarwa, an ga matasan ‘yanhoho da itace suna ihun basa so da sauransu.