
Matar shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta bayyana cewa, fina-finan Nollywood da kafafen sada zumunta da ‘yan Najeriya ke ta’ammuli dasu ne ke zuga da wa wajan son yin kudi dare daya.
A cikin abubuwan da take suna zuga mutane dan neman kudin dare daya hadda Addini.
Tace Hakan ne ma yake sa ake safarar mutane inda tace tana baiwa hukumar hana safarar mutane gwarin gwiwa akan aikin da take.
Ta bayyana hakane yayin da shugabar NAPTIP Binta Bello ta kai mata ziyara a ofishinta dake fadar shugaban kasa a Abuja.
Me taimakawa matar shugaban kasar ta bangaren yada labarai, Busola Kukoyi ce ta bayyana haka a wata sanarwa data fitar inda tace Matar shugaban kasar ta bada shawarar a rika karfafa mutane dan su rika yin aiki tukuru da kuma hakuri da rayuwa.