
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su rage sukar da suke masa maimakon hakan, su rika gode masa.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara ta musamman akan mazabu, Khadija Omotayo inda ta wakilceshi a Birnin Jos na jihar Filato wajan taron karawa juna sani da ya gudana a ranar Asabar.
Khadija tace, shugaban kasar ya cire tallafin man fetur ne dan amfanin kowa, domin kuwa kudaden da aka samu daga cire tallafin man fetur din an rabasu ga kowace jiha ta hannun gwamnoni.
Tace shugaban kasar ya kuma karawa ma’aikata Albashi sannan yace zai kara yin wani karin, tace gashi ya turata ta wakilceshi a taron a jihar da Jam’iyyar PDP ke shugabanci wanda hakan na nuna bashi nuna wariya kowa nashine, tace dan haka shugaban ya cancanci yabo.
Khadija ta kuma baiwa matasa shawarar da su yi amfani da damar samun bashi da shugaban ya kawo ga dalibai dan cimma burikansu na karatu.