Wednesday, April 8
Shadow

Mafi yawancin Gwamnoni na barin jihohinsu ne su je Abuja su tare>>Inji NLC

Shugaban kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajero ya koka da cewa, mafi yawanci gwamnonin Najeriya kan bar jihohinsu su je Abuja su tare.

Yace hakan na faruwane a yayin mutanen jihohin wadannan gwamnonin ke fama da wahalar rayuwa.

Ya bayyana hakane a wajan taron karawa juna sani da ya faru a Lokaja jihar Kogi.

Ajaero ya bayyana cewa, sun ziyarci yankuna 5 na Najeriya amma mafi yawanci duk sun iske gwamnonin basa nan sun tafi Abuja.

An yi taron na NLC ne a Lokoja dan ma’aikatan jihar su bayyana matsalolinsu dan a kaiwa Gwamnan jihar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Karya kuke, Wannan ba Samha M. Inuwa bace, baba Tambayace>>Inji Gfresh bayan da wadannan hotuna na Samha M. Inuwa ke ta yawo a kafafen sada zumunta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *