Sunday, March 16
Shadow

Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan Hakar ma’adanai saboda matsalar tsaro

Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan hakar ma’adanai saboda magance matsalar tsaro dake karuwa a jihar.

Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ne ya bayyana hakan a wata sabuwar doka da ya sakawa hannu.

Yace wannan mataki ya zama dole saboda yanda ake samun karuwar matsalar tsaro a jihar da suka hada da garkuwa da mutane da sayar da kwayoyi da shigowar ‘yan kasar waje da sauransu.

Ya bayyana cewa, dokar zata fara aiki ne ranar Juma’a 21 ga watan Janairu.

Sannan yace daga yanzu sai wanda aka baiwa lasisin zasu rika hakar ma’adanai a jihar.

Karanta Wannan  Allah ka kara min Talauci>>Inji Wannan matashin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *