
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a shekarar 2031 bayan Tinubu ya gama Mulki.
Yace shiyasa ma Nuhu Ribadun ya hada kai da gwamnan Kaduna na yanzu, Malam Uba Sani dan bata masa suna.
El-Rufai ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Inda ya kara da cewa amma kokarin na bata masa suna yana basu wahala.