Sunday, May 18
Shadow

Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana’a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar cewa su raba kafa, kada su tsayawa sana’a daya.

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV.

Yace ba zai yiyu mutum ya tsayawa sana’a ko aiki daya ba.

Yace misali idan akwai gona a kusa da inda kake, sai ka dan yi noma dan samun saukin rayuwa.

Ya karkare da cewa ya kamata mutane su samarwa kansu mafita.

Karanta Wannan  Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *