Friday, December 5
Shadow

Kotu ta daure matashi da ya saci Kaza

Kotun Magistrate dake Ago Iwoye, a jihar Ogun ta daure wani matashi me suna Adebanjo Segun dan kimanin shekaru 21 saboda satar kaza.

Kakakin Hukumar NSCDC na jihar, Dyke Ogbonnaya ne ya sanar da hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Laraba.

Lamarin ya farune ranar Laraba, February 19, 2025 inda aka kama matashi Adebanjo.

Ogbonnaya ya bayyana cewa, Matashin ya taba aikata hakan a watan Disamba na shekarar 2024 amma aka yafe masa da tunanin cewa shine na farko da ya taba aikatawa.

Yace amma a wannan karin an gurfanar dashi a kotu inda kotun ta yanke masa hukuncin daurin watanni 6.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Abin takaici ne yanda aka baiwa 'yan mata 'yan kwallon Najeriya kyautar Naira Miliyan 160, kudin da har soja ya gama aikinsa in za'a hada duka abinda zai samu ba zai kai hakan ba>>Soja ya koka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *