Saturday, June 27
Shadow

Ana zargin Mawakin Najeriya, Burna Boy ya yaudari wannan budurwar me suna Sophia Egbueje yayi lalata da ita da sunan cewa zai sai mata motar Lamborghini amma bai cika mata alkawari ba

Maganganu na ta yawo cewa, shahararren mawakin Najeriya, Burna Boy ya yaudari wata babbar yarinya da take wuta a birnin Legas me suna Sophia Egbueje inda yayi lalata ita da sunan zai sai mata motar Lamborghini amma bai cika mata alkawari ba.

Yanda aka san labarin shine Sophia ta baiwa kawarta labarin abinda ya farune inda kuma hirar tasu ta watsu a kafafen sadarwa.

A cikin muryar da aka nada, an ji Sophia na bayar da labarin cewa, sun gama rawa da Burna Boya a gidan rawa inda ya kaita gidansa ya kasheta da kalamai ita kuma ta yadda yayi lalata da ita da sunan zai sai mata motar.

Karanta Wannan  Kasar Japan zata gina Lifter wadda zata rika kai mutane sauran duniyoyi dake wajen Duniyar mu dan su ga yanda al'amura ke gudana

Tace daga baya ma kwata-kwata ya daina kiranta.

Tuni dai akai ta mayar da martani kan lamarin inda da yawa suka rika mata dariya da kiranta marar wayau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *