
Sojojin Najaria da suka yi ritaya sun bayyana cewa abune me wuya a iya hana mutanen kauyuka ci gaba da biyan ‘yan Bindiga kudin fansar danginsu da aka kama ko kuka kudin Harajin da ‘yan Bindiga suka kakaba musu.
‘Yan Bindiga kan kakaba Haraji me yawa tsakanin Naira Miliyan 20 har zuwa naira Miliyan 200 ga kauyuka au tursasa mutane biya ko kuma su kai hari garin.
A watan July na shekarar 2024, ‘yan Bindiga sun kakabawa mutanen garin Toro dake jihar Benue harajin Naira Miliyan 20 inda kowane gida a kauyen sai da ya biya Naira Dubu 50 aka tattara kudin.
Hakanan a watan Satumba na shekarar 2024 Bello Turji ya kakabawa garin Moriki na karamar hukumar Mulki ta Zurmi dake jihar Zamfara harajin Naira Miliyan 30.
Hakanan a watan Janairu na wannan shekarar, 2025 da muke ciki akwai wani dan Bindiga me suna Dantsito da ya kakabawa mutanen Tsafe dake jihar Zamfara harajin Naira Miliyan 200.
Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta sha gargadin ‘yan Najeriya da su daina baiwa ‘yan Bindigar irin wadannan kudade amma mutane basu iya dainawa.
Da yake magana akan lamarin, tsohon soja, Gen. Ishola Williams (retd.), ya bayyana cewa babban abinda ke sa mutane biyan irin wadannan kudaden haraji shine basu yadda da sojoji ba.
Yace mutane basu da kwarin gwiwar cewa sojiji zasu karesu shiyasa suke biyan kudin harajin da ‘yan Bindigar ke kakaba musu yace amma da sun san sojojin zasu iya basu kariyar data dace da babu wanda zai rika biyan kudin Harajin.
Hakanan shima, Brig. Gen. John Sura (retd) ya bayyana cewa matsalar itace sojojin ba zasu iya kasancewa suna kai dauki da sauri ba dole sai mutane suma sun tashi tsaye sun baiwa kansu kariya.
Yace yawanci ana ajiye sojoji ne a kananan hukumomi wanda suna da nisa da inda sojojin suke su kuwa wadannan ‘yan Bindigar sun fi kusa da mutane dan haka dole mutane tunda an fi karfinsu su rika biyan kudin fansar.
Yace a jihar Benue mutane sun samu masu tsaro na sa kai hakanan a jihar Bauchi ma inda sai da mutanen wani kauye sukawa ‘yan Bindigar mummunar illar da basu sake kai musu hari ba.
Yace irin wadannan matakai ne ya kamata mutane su rika dauka dan baiwa kawunansu kariya.