Saturday, March 15
Shadow

Talauci da rashin tsaro ya karu a Najeriya>>Inji Kungiyar Kiristoci darikar Katolika

Kungiyar Limaman Kiristoci na darikar Katolika sun bayyana cewa matsalar talauci, rashin aikin yi tsakanin matasa da matsalar tsaro na karuwa a Najeriya.

Kungiyar ta bayyana hakane a zaman ta a Abuja ranar Labadi inda ta nemi shugaba Tinubu da ya dauki matakin gyara.

Zaman wanda ya samu halartar shugabannin Kungiyar Most Rev. Lucius Ugorji, Archbishop na cocin Owerri da shugaban CBCN, Archbishop Daniel Okoh, da kuma shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Christian Association of Nigeria (CAN); da Most Rev. Ignatius Kaigama, Catholic Archbishop of Abuja ya yi na’am da matakan Gwamnati na gyara amma yace matakan sun yi kadan.

Karanta Wannan  Yajin aiki akan kara kudin kiran waya ba gudu ba gudu ba ja da baya>>TUC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *