
Jihar Kebbi ta gabo karin ma’adanai na karkashin kasa a jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Yakubu Ahmed-BK ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace an gano karin ma’adanan ne a Jega, Dandi, Gwandu, Suru, Birnin Kebbi, Argungu da sauransu.
Wannan na zuwane a yayin da jihar Kebbi ke da ma’adanai kamar su gwal da sauransu.
Ya bayyana gano wadannan karin ma’adanai da cewa, wata hanyace ta karin samun kudin shiga ga jihar.