
Yaro dan shekaru 14 ya mutu wasu mutane 21 suka jikkata bayan da tukunyar gas ta fashe a Goron Dutse dake Jihar Kano.
Lamarin ya farune da misalij karfe 2:30 na rana a gidan Malam Isiyaka Rabiu yayin da tukunyar gas din ta fashe a dakin girki.
Rahoton yace wuta ta kama bayan fashewar gas din.
Tawagar ‘yansanda bisa jagorancin ACP Nuhu Mohammed Digi ta kai dauki inda lamarin ya faru.
An kai wadanda suka jikka zuwa asibitocin Gamji Hospital, Dala Orthopaedic Hospital, da Murtala Mohammed Specialist Hospital dan kula dasu.
‘Yansandan sun mika sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan wanda ya rasu.