
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata saka ido akan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan da ya canja Jam’iyya daga APC zuwa SDP.
Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin me baiwa shugaban kasar shawara kan yada labarai, Daniel Bwala.
Bwala yace basu da matsala da El-Rufai akan canja Jam’iyya.
Amma barazanar da yake musu ta cewa, zai hada kan ‘yan adawa dan su taru su hana APC cin mulki a shekarar 2027 yasa dole su saka ido akansa.
El-Rufai yace banbancinsu da APC abu ne wanda ba zai taba sa su sami jituwa ba shiyasa ya fice daga Jam’iyyar.