Saturday, May 17
Shadow

Wata Sabuwa:Ana rade-radin an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shiga fadar shugaban kasa har hakan tasa fadar shugaban kasar yin magana

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shiga fadar shugaban kasar dake Abuja.

Saidai a martanin da fadar shugaban kasar ta fitar ta bakin me magana da yawun shugaban kasar, Stanley Nkwocha yace wannan magana karyace da wasu suka kirkira dan cimma wata manufa.

Ya kara da cewa babu wani abu me kama da wannan da ya faru a fadar shugaban kasar.

Yace hankalin mataimakin shugaban kasar na kan aikin da yake gabansa na gina kasa.

Hakanan ya kawo bayanai akan wata karya da aka yada a baya ta fastar yakin neman zaben shugaban kasar da mataimakinsa wanda yace basu da alaka dashi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Baban Dan Bello ya taba zuwa sata a Kabari, tun daga nan ne ya bar garinsu na Galadanci ba'a sake jin duriyarsa ba saboda Abin Kunya>>Inji Murtala Gamji, Shugaban dattawan Matasan Najeriya wanda ya fito kare Shaikh Bala Lau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *