Thursday, February 5
Shadow

A kama Fasto da ya dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki, ya amsa laifinsa

A jihar Ondo Hukumomi na binciken wani fasto me suna Peter James saboda zargin dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki.

Yarinyar dai na daya daga cikin mas wake-wake a cocinsa.

Lamarin ya farune a garin Oke-Gburowo, dake karamar hukumar Odigbo, ta jihar.

Da farko dai jami’an Amotekun ne suka kama faston inda aka kaishi fadar sarkin garin kuma bayan gabatar masa da zargin da ake masa, ya amsa laifinsa

Saidai daga baya ya murzawa idanunsa kwalli yace cikin ba nashi bane.

Mahaifiyar yarinyar me suna Mrs. Victoria Bernard tace faston ya ki amsa laifinsa ne saboda yaga yarinyar na da nakasa.

Ta yi kira ga hukumomi da su amsar musu ‘yancinsu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ina da Karama, Kuma ina gaya muku ko dai a taso a taimaka mana wajan kokarin kawo zaman lafiya da muke a Arewa ko kuma abinda za'a gani nan gaba sai yafi abinda ake ciki yanzu>>Inji Sheikh Musa Asadussunnah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *