Sunday, January 5
Shadow

WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya’a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi

WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya’a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi

Sayyadi Muktar Ibrahim Dahiru Bauchi ya musanta labarin da wasu jaridu suka wallafa cewar sun je sun yi wa Sarki Sunusi II mubaya’a sannan suka kara yi wa Sarki Aminu Ado Bayero mubaya’a.

A cewar sa sun kai ziyarar ne karkashin wata kungiya da Sheikh Aminu Dahiru Bauchi ke jagoranta na hadin kan al’umma musulmi tare da samar da cigaba, inda daga nan suka kuma kaiwa Sarki Aminu ziyara domin jajantawa akan abun da ya faru da shi.

“Mu ba mu dauki bangare ba, kawai muna fatan Allah ya kawo dauki ne akan abun da ke faruwa a Kano, domin duk wani Musulmi a Arewa ba zai ji dadin abun da ke faruwa ba a Gidan Dabo”, inji SayyadiMukhtar Ibrahim Sheik Dahiru Bauchi.

Karanta Wannan  Kowane Musulmi Imaninsa Yana Cika Ne Idan Ya Yarda Tare Da Rungumar Kowace Irin Kaddara Ce Ta Same Shi, Cewar Sarki Sanusi II A Hudubarsa Ta Yau Juma'a

Daga Nuruddeen Isyaku Daza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *