Monday, May 19
Shadow

Ji Yanda Tsohon Ministan Sufuri Amaechi ya bayar da labarin yanda Allah ya tuka motarsa bayan da bacci ya kwasheshi yana tsaka da tuki daga Kaduna zuwa Abuja

Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayar da labarin cewa, akwai sanda ya tuka mota daga kaduna zuwa Abuja yana bacci inda yace allah ne ya tuka motar ya kaisu Abuja lafiya.

Ya ce a lokacin sun je Kanone sun nada sarki, zasu koma sai aka hana sayar musu da tikitin jirgin sama.

Yace sai ya kira tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar dashi inda Kwankwason yace masa ya je gidan gwamnatin jihar.

Saidai yace a yayin da yake shirin tafiyane sai shugabab DSS na Kano ya sameshi yace masa duk abinda yake ciki ya fice daga garin Kano dan ba zai iya bashi tabbacin kariyar rayuwarsa ba.

Karanta Wannan  An sake Kai wani mummunan hari jihar Filato

Yace ya gayawa shugaban DSS din yanda suka yi da Gwamna, yace masa amma kada ya sake ya je gidan gwamnatin, su fice daga Kano kawai.

Amachi yace tare dashi akwai Goje, Baraje da Professor Gambari, yace haka suka samu mota suka zuba mai suka kama hanyar zuwa Kaduna.

Yace duk ukun bacci ya kwashesu sai shi kadai yana ta tuki.

Yace da suka je Zaria ya sauka ya sayi lemun Red Bull guda 6 saboda ya fara jin bacci shima amma duk da haka basu hanashi bacci ba.

Yace haka yayi ta bacci yana tuki, Allah ne ya tuka motar daga Kaduna zuwa Abuja ya kaisu Lafiya.

Karanta Wannan  Ku baiwa Zuciyarku hakuri ko tana so ko bataso ku sake zaben mu, saboda mu samu kammala gyaran da muka fara, idan kuka zabi wani shugaban kasa, ba Tinubu ba, za'a samu babbar matsala dan zai dakatar da duka ayyukan ci gaban da ya fara ne>>Gwamnatin Tinubu ta roki 'yan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *