Friday, December 5
Shadow

Karya Ake Min:Bance Na yi nadamar yin takara da Atiku ba, cewa na yi na gano mutanen mu basa son dan Arewa>>Inji Wanda yawa Atiku takarar mataimakin shugaban kasa Ifeanyi Okowa

Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa wanda ya koma APC yace ba’ masa Adalci ba labarin da aka rika yadawa wai yace yayi dana sanin yiwa Atiku takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Okowa yace shi bai fadi haka ba, yace abinda ya fada a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV shine, ya lura mutanensa basa son zaben dan Arewa, dan kudu suke son zaba.

Yace amma duk da haka bai ki ci gaba da takara da Atiku ba.

Okowa ya bayyana hakanne ta bakin tsohon kakakinsa wanda a yanzu shine kakakin gwamnan jihar Delta, Mr Olisa Ifeajika inda yace ‘yan jaridar da suka wallafa wancan labarin basu wa Okowa Adalci ba.

Karanta Wannan  Akwai Wanda Ya Yi Minista Mai Lasisi Amma Ba Za Ka Nuna Masallaci Guda Daya Da Ya Gina A Jihar Gombe Ba, Ko Yake Daukar Nauyin Wasu Limamai Ko Ladanai Ba, Cewar Sheik Albanin Gombe, ko kun san da wa yake?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *