Saturday, December 13
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Karon Farko Nijeriya Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani

DA ƊUMI-ƊUMI: Karon Farko Nijeriya Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani.

Rahotanni da ke shigo mana yanzu sun tabbatar da cewa Nijeriya za ta karɓi bakwancin masabaƙar karatun Alkur’ani mai girma ta duniya a wannan shekarar.

Majiyar Jaridar Arewa ta tabbatar da cewa Musabaƙar ta ƙasa da ƙasa wadda za a gabatar a watan Agustan bana 2025.

Tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bassa a Jihar Filato, Muhammad Adam Alkali, ya ɗauki nauyin shirya wannan gasar. Hakazalika za a fara daga Jos ne, daga bisani a kammala a birnin Abuja.

Ana kyautata zaton Musabaƙar zata samu halartar wakilai daga ƙasashe kusan 20, na sassan faɗin duniya.

Karanta Wannan  Akwai Wanda Ya Yi Minista Mai Lasisi Amma Ba Za Ka Nuna Masallaci Guda Daya Da Ya Gina A Jihar Gombe Ba, Ko Yake Daukar Nauyin Wasu Limamai Ko Ladanai Ba, Cewar Sheik Albanin Gombe, ko kun san da wa yake?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *