
Wasu majiyoyi daga kafar The Blaze sun bayyana cewa, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na shirij daukar wani sabon mataki dan baiwa Kiristocin Najeriya kariya.
Rahoton yace, shugaba Trump na shirin daukar matakinne a asirce ba kamar a baya ba yanda ya rika yayatawa ba.
Rahoton yace shugaban Amurka, Donald Trump ya fahimci cewa Najeriya na da muhimmanci sosai a nahiyar Afrika kuma duk wanda ya mallaketa ko ya iya juya akalarta, Kamar yana juya akalar gaba dayan Nahiyar Afrika ne.
Dan hakane hankalinsa ya koma kan Najeriya.
Najeriya tana daga cikin manyan kasashe 5 na kungiyar kasashen dake fitar da danyen man fetur, watau, OPEC, sannan tana da ma’adanan kasa da suka haura dala Tiriliyan wanda ba’a ma fara fito dasu ba.