Friday, January 23
Shadow

Munin Tattalin arzikin Najeriya a yanzu yafi na lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yanci a shekarar 1960>>Inji Shugaba Bankin Afrika

Shugaban bankin Afrika, AFDB, Dr Akinwumi Adesina ya bayyana cewa, lalacewar tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya fi muni fiye da lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yancin kai a shekarar 1960.

Ya bayyana hakanne a wajan wani taro da ya faru a Legas ranar Alhamis.

Yace Abinda ake cewa GDP per capital wanda shine ake auna ma’aunin tattalin arzikin kasa dashi a yanzu yana kan Dala $824 ne.

Yace a yayin da a lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yancin kai a shekarar 1960 GDP per Capital yana kan Dala $1,847 ne.

Yace hakan ba karamar matsala bace inda yace ya kamata Gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye dan shawo kan wannan matsalar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Da Rarara da Sarkin Waka duk 'yan girman kai ne, babu me dama-dama a cikinsu>>Inji Sheik Sani Isah Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *